A cikin wani faifan bidiyo da ‘yan kungiyar suka fitar da suka ba shi taken “Sako Ga Kawayen Amurka”, sun nuna yadda suka yanka jami’in agaji a matsayin mayar da martani ga abin da suka kira hadin kan da Birtaniyyan take ba wa Amurka a hare-haren da ake kai musu a Iraki, suna masu barazanar yanka wani dan kasar Birtaniyan da ke hannunsu.
Firayi ministan Birtaniya David Cameroon ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin da ya kira ‘tsagoron mugunta’ yana mai alwashin ci gaba da neman wadanda suka aikata hakan don hukumta su. Shi ma shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nuna damuwarsa ga abin da ya kira ‘kisan gillan rashin imani’ yana mai sake jaddada aniyarsa ta aiki da gwamnatin Birtaniyya wajen kawo karshen kungiyar ta ISIS a cewarsa.
A watan Maris na shekara ta 2013 ne ‘yan kungiyar ta Da’ish suka kama Mr. Haine a kasar Siriya da kuma barazanar sare kansa. Kafin yanka shi din dai Mr. Haine ya zargi gwamnatin Birtaniyyan da gazawa wajen ceto ransa yana mai Allah wadai da hadin kan da take ba wa Amurka. ABNA